Monday, April 6, 2026
HomeKetareShugaba Trump ya yi sabuwar barazanar kara kawo sabbin hare-hare a Nijeriya

Shugaba Trump ya yi sabuwar barazanar kara kawo sabbin hare-hare a Nijeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin barazanar sake kai hare-haren a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci, duk da musanta wa da gwamnatin Nijeriya.

Trump, ya bayyana cewa Amurka na iya kara kai hare-haren soji a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci a kasar, kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito a wata hira da aka wallafa ranar Alhamis, 8 ga Janairu 2026.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters,ya rawaito cewa Trump ya yi wannan jawabi ne yayin da ake tambayarsa kan harin soji da Amurka ta kai Nijeriya a ranar Kirsimeti, inda sojojin Amurka suka ce sun kai harin ne kan ‘yan kungiyar IS a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya bisa bukatar gwamnatin Nijeriya.

Trump ya kara da cewa duk da cewa Musulmi ma ana kashe su a Nijeriya, a cewarsa Kiristoci ne suka fi fuskantar hare-hare, ra’ayin da gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da shi, tana mai jaddada cewa ‘yan ta’adda na kashe Musulmi da Kiristoci baki daya, ba tare da nuna wariya ta addini ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata