Shugaban Jamhuriyar Congo, Denis Sassou Nguesso, ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara a zaben shugaban ƙasa da za ayi 15 ga Maris.
A yanzu dai yana da shekaru 82, kuma ya jagoranci ƙasar mai arzikin man fetur na tsawon shekaru 42, wanda ya zama ɗaya daga cikin shugabannin Afirka da suka dade a kan mulki bayan Paul Biya na Cameroon da Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea.
Sassou Nguesso ya yi wannan sanarwar ne gaban dimbin al’umma a karamar hukumar Ignie, inda ya yi alkawarin inganta tsaron abinci da tallafawa matasa.
