Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiShugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga Abuja a ziyarar da...

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga Abuja a ziyarar da zai kai kasashen Japan da Brazil

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa kasashen Japan da Brazil domin halartar taro da kuma ziyarar aiki.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga, Tinubu zai fara tsayawa a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ya wuce Japan.

Shugaban kasar zai halarci taron kasa da kasa karo na 9 kan cigaban Afirka (TICAD9) a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta, za a gudanar da taron ne domin tattauna batutuwan cigaban Afirka, inda Tinubu zai shiga zaman tattaunawar kuma zai gana da shugabannin kamfanoni masu zuba jari daga Japan a Najeriya.

Bayan kammala taron, shugaban Najeriya zai wuce Brazil daga ranar Lahadi 24 zuwa Litinin 25 ga watan Agusta, bisa gayyatar shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata