Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiFicewar Atiku daga PDP ya saba faruwa, muna sa ran zai dawo - Damagum

Ficewar Atiku daga PDP ya saba faruwa, muna sa ran zai dawo – Damagum

Shugaban riko na jam’iyyar PDP Ambasada Iliya Damagum, ya bayyana ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, daga jam’iyyar a matsayin wani lamari da ba sabon abu ba.

Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi ranar Juma’a, Damagum ya ce jam’iyyar PDP ba ta ji wani mamaki ko damuwa ba dangane da ficewar Atiku, domin ya saba da irin wannan a shekarun baya.

“Yana cikin tsarin da muka saba da shi — ya tafi, ya dawo. Wannan wani salo ne na siyasarsa, ba mu ɗauke shi a matsayin rabuwa ta dindindin ba,” in ji Damagum.

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa Atiku na ƙoƙarin shiga jam’iyyar hadaka ta ADC a hukumance, a shirin tunkarar zaɓe mai zuwa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata