Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiSojoji 18 da ‘Yan Sanda 15 sun shiga hannu kan harkallar makamai...

Sojoji 18 da ‘Yan Sanda 15 sun shiga hannu kan harkallar makamai a Jihohi 11 – Rundunar Tsaro

Rundunar Operation Hadin Kai ta kama sojoji 18 da ‘yan sanda 15 bisa zargin sayar da makamai ga ‘yan ta’adda a wani samame da aka gudanar a jihohi 11 karkashin shirin Operation Snowball.

Jaridar Punch ta ruwaito kakakin rundunar, Manjo Ademola Owolana, ya ce an kama su ne a Bauchi, Benue, Borno, Ebonyi, Enugu, Lagos, Plateau, Kaduna, Rivers, Taraba da Abuja.

Haka kuma an damke fararen hula 8 da wani basarake, ciki har da Ameh Raphael, wanda ake zargin da safarar makamai tun 2018, inda aka gano N45m a asusunsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata