A ranar Alhamis, rundunar sojin Guinea-Bissau ta sanar da cewa an rantsar da Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban rikon kwarya, kwana guda bayan da suka hambarar da gwamnatin kasar.
A cewar sanarwar da sojin ƙasar suka fitar, rantsuwar ta biyo bayan jawabin da hafsoshin rundunar suka yi tun a ranar Laraba inda suka bayyana cewa sun kifar da shugaban ƙasar da ke kan mulki.
Rahotanni daga France24 sun bayyana cewa wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tashe-tashen hankula a yankin Yammacin Afirka, musamman game da karuwar juyin mulki a wasu kasashe.
