Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiSojoji na dab da yi wa Bello Turji 'Ƙofar Raggo' - Rundunar...

Sojoji na dab da yi wa Bello Turji ‘Ƙofar Raggo’ – Rundunar sojin Nijeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce nan ba dadewa ba ƙasurgumin dan ta’adda Bello Turji zai zo hannu.
Jami’in yada labaran rundunar ta operation Fansar Yamma Laftanal Kanal Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da makaman da rundunar ta ƙwace daga ‘yan bindiga a karamar hukumar Kaura -Namoda dake jihar Zamfara.
Abubakar ya ce Turji na cigaba da wasan buya tsakaninsa da rundunar, sai dai ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya rundunar za ta kamo shi.
Jami’in ya yaba tare da godewa al’umma bisa hadin kai da bayanan sirri da suke bai wa rundunar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata