Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea-Bissau sun ce za a gudanar shugaban ƙasa a ranar 6 ga Disambar 2026, bayan da suka kifar da tsohon shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo, a ƙarshen 2025.
Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta rawaito cewa shugaban mulkin sojin ƙasar, Manjo-Janar Horta Inta-a, ya sanar da hakan ne a wata doka da aka sanar a ranar Laraba, inda ya ce an cika dukkan sharuddan gudanar da zaɓen cikin ‘yanci, adalci da gaskiya.
Rahoton ya bayyana cewa juyin mulkin da ya faru a watan Nuwamba ya kawar da Embalo, tare da naɗa Horta Inta-a don jagorantar gwamnatin na tsawon shekara guda.
