Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiSojojin Nijeriya za su murƙushe ‘yan ta’addan Lakurawa — Babban hafsan sojin...

Sojojin Nijeriya za su murƙushe ‘yan ta’addan Lakurawa — Babban hafsan sojin kasa Janar Waidi Shaibu

Babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya sha alwashin murƙushe sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa wadda ke addabar wasu sassan arewacin Nijeriya.

Janar Shaibu, wanda Shugaba Tinubu ya nada kwanan nan, ya bayyana haka ne yayin da Majalisar Dattawa ke tantance shi a Larabar nan.

A cewar sabon hafsan sojin, yana da gogewa a fagen yaki da ta’addanci tun lokacin da ya jagoranci sojoji a jihar Borno, inda ya ce a lokacin sunci karfin Boko Haram, kuma da dama daga cikinsu sun miƙa wuya.

Ya kara da cewa, sun yi amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan soji, wanda hakan ya taimaka wajen lalata ƙungiyoyin ta’addanci da dama.

Janar Shaibu ya kuma bayyana cewa nan gaba, rundunar soji za ta mayar da hankali wajen ci gaban ma’aikata da kula da jin daɗinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata