Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiSojojin rundunar hadin kai sun yi ajalin mayaka 24 cikin kwanaki 6...

Sojojin rundunar hadin kai sun yi ajalin mayaka 24 cikin kwanaki 6 a Arewa maso Gabas

Dakarun hadin gwiwa na Operation Hadin Kai sun yi ajalin ‘yan ta’adda 24 na Boko Haram da ISWAP a wani sabon samame da suka kai maboyarsu a sassa daban-daban na yankin Arewa maso Gabas.

Daga cikin wadanda aka kawo karshensu har da masu kai musu kayan abinci da makamai guda 5 da dakarun suka yi wa kwanton-bauna da daddare.

Samamen ya gudana ne tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli, a wurare kamar dajin Sambisa, yankin Timbuktu triangle, da tsaunukan Mandara, inda aka kwato bindigu, harsasai, da kayan yaki.

Rahoton da gidan talabijin na Channels ya ruwaito sojojin sun kuma kwato babura, keken hawa, kayan abinci, takalma da kayan sojojin da ‘yan ta’addan ke aiki da su, a kokarin murkushe ragowar mayakan a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata