Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiSojojin saman Najeriya sun lalata maboyar 'yan bindiga a Borno

Sojojin saman Najeriya sun lalata maboyar ‘yan bindiga a Borno

Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa jerin hare-haren da dakarunta suka kaddamar, ya yi sanadiyyar hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata maboyarsu a jihar Borno.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Air Commodore Ehimem Ejodame ya fitar a Abuja, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce dakarun karkashin shirin Operation Hadin Kai, sun kai farmakin ne a yankunan Bula Madibale da Gezuwa da ke jihar.

Kazalika ya ce an kaddamar da hare-haren ne bayan samun bayanan sirri na taruwar ‘yan ta’addan a yankunan daga sassa daban daban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata