Thursday, April 9, 2026
HomeSiyasaTaron sulhunta PENGASSAN da matatar Dangote ya koma ofishin NSA

Taron sulhunta PENGASSAN da matatar Dangote ya koma ofishin NSA

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa taron sulhu tsakanin shugabannin ƙungiyar ma’aikatan PENGASSAN da kuma jagorancin matatar man fetur ta Dangote an mayar da shi zuwa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro NSA.

Rikicin ya samo asali ne daga matsalolin kwadago da ba a warware ba tsakanin ɓangarorin biyu.

Ministan kwadago da ayyukan yi, Mohammed Dingyadi, tare da wasu daga cikin shugabannin PENGASSAN da suka isa wurin taron tun farko, sun bar wajen inda suka nufi ofishin NSA inda ake gudanar da tattaunawar.

Yanzu haka dai taron na gudana ne a cikin sirri, kamar yadda rahotanni suka bayyana

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata