Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiTattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 - IMF

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2025 da 3.2% a 2026.

Wannan sabon rahoto na World Economic Outlook da aka fitar a watan Yuli 2025, ya fi hasashen da aka yi a watan Afrilu na 3.0% da 2.7%.

IMF ta kuma kara hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya gaba ɗaya zuwa 3.0% a 2025 da 3.1% a 2026, yayin da yankin Sub-Saharan Africa zai kai 4.0% a 2025 da 4.3% a 2026.

Sai dai, IMF ta shawarci kasashen yankin su dauki matakan gaggawa na gyaran tsarin mulki da hukumomi, duba da kalubalen tattalin arziki da suke fuskanta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata