Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya nuna damuwa kan yawaitar lalata kayayyakin wuta da ake yi a wasu yankunan Kudu maso Gabas, musamman a Agbogugu da Ihe na karamar hukumar Awgu a jihar Enugu.
Shugaban TCN na yankin Enugu, Dr. Thomas Inugonum, ya ce matsalar tana janyo asarar kayan aiki da katse wuta, yayin da kamfanonin rarraba wuta (DISCOs) ke jingina gazawarsu da lalata layukan lantarki.
Rahoton jaridar The Nation yace an bukaci shugabannin gargajiya da matasa su taimaka wajen kare kayayyakin wuta, yana mai cewa TCN tana da isasshiyar wuta a tashoshinta, amma DISCOs na gaza rarrabawa.
