DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeSiyasaTinubu ba shi da niyyar ci gaba da mulki bayan 2031 –...

Tinubu ba shi da niyyar ci gaba da mulki bayan 2031 – Martanin fadar shugaban Nijeriya ga El-rufa’i

Fadar shugaban Nijeriya ta tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da wani shiri na zarcewa kan mulki bayan 2031 idan ya sake lashe zaben 2027, tana mai jaddada cewa shugaban kasa na tsayawa tsayin daka kan bin ka’idojin dimokuraɗiyya.

Wannan na zuwa ne biyo bayan wan furuci da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya zargi gwamnatin Tinubu da yin kama karya, tare da kwatanta shi da shugaba Paul Biya na Kamaru wanda ya ke mulki tun daga 1982.

Sai dai a martaninsa, mai ba shugaban kasa shawara na musamman, Bayo Onanuga, ya bayyana furucin El-Rufai a matsayin zargi maras tushe da kuma abin dariya.

Ya ce shugaba Tinubu yana girmama dimokuraɗiyya kuma ba shi da niyyar ci gaba da mulki bayan karewar wa’adinsa na biyu a karshen Mayun shekarar 2031.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata