Wednesday, April 8, 2026
HomeSiyasaTinubu bai shirya gudanar da sahihin zabe a 2027 ba - Buba...

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zabe a 2027 ba – Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP a Najeriya Buba Galadima, ya zargi gwamnatin shugaba Tinubu da yunkurin kaucewa gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027.

Buba Galadima ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Arise, inda ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu ta sanya gwamnatocin jihohi a karkashin ikonta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar sa, gwamnatin na taka rawa wajen kawo hargitsi a cikin jam’iyyun hamayya, tare da cewa ya jiyo rade-radin shugaba Tinubu zai sauya shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, inda ya yi gargadi kan hakan.

A bangare guda, ya soki hukumar ta INEC kan yadda ya ce ta gaza daukar mataki kan masu gudanar da yakin neman zabe tun kafin lokacin da doka ta tanada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata