Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiTinubu ya aika da sunan Dr. Bernard Mohammed ga majalisa don nada...

Tinubu ya aika da sunan Dr. Bernard Mohammed ga majalisa don nada shi minista

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Dr. Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato ga majalisar dattawa don nada shi minista a gwamnatinsa.

Bayanin aike wa da sunan na sa na kunshe cikin sanarwa da fadar gwamnatin Tinubu ta fitar.

Dr. Bernard Mohammed Doro dai ya kasance kwararre a bangaren lafiya, inda ya samu gogewa ta tsawon shekaru yana aiki a fannin a ciki da wajen Nijeriya.

Wannan ya zo ne bayan da aka zabi Farfesa Nentawe Yilwatda daga jihar ta Filato a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata