DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ba da umarnin samar da hanyoyin rage tasirin raɗaɗin rikicin...

Tinubu ya ba da umarnin samar da hanyoyin rage tasirin raɗaɗin rikicin gabas ta tsakiya ga ƴan Najeriya

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci manyan jami’an tattalin arzikin Najeriya da su gaggauta fito da matakan da za su rage wa talaka radadin da rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya ya jefa shi a ciki.

Shugaba Tinubu ya bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a, yayin wata liyafa da aka shirya masa a birnin Yenagoa, bayan ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Douye Diri ya samar a Jihar Bayelsa.

Tinubu ya dora wa Ma’aikatar Kudade da ta Tsare-tsare, tare da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, nauyin duba hanyoyin da za a saukaka wa ‘yan kasa halin matsin tattalin arziki.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya fitar daga birnin Yenagoa, Shugaban ya amince cewa lallai rikicin duniya ya janyo tsadar rayuwa, musamman ta fuskar farashin man fetur da ke addabar jama’a.

“Ina jin koke-kokenku ta kowane bangare na tattalin arziki. Farashin mai na ratsawa, amma dole mu yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya,” in ji Tinubu.

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa mai kula da jin dadin jama’a ce, kuma za ta zauna da masana domin fito da lissafin da zai saukaka wannan nauyi da ya danne kafadar talaka.

Haka zalika, ya jaddada aniyar jam’iyyar APC na inganta jin dadin jama’a ta hanyar ayyukan raya kasa da ke taba rayuwar talaka kai-tsaye.

“Mutane na bukatar ganin an fassara mulki ta hanyar hanyoyin mota, gadoji, wutar lantarki, da samar da ayyukan yi,” in ji shi.

A yayin ziyarar, Shugaban ya kaddamar da wasu gagaruman ayyuka a jihar, ciki har da tashar samar da wutar lantarki ta ‘gas’ mai karfin megawat 60 a kauyen Elebele, da gadar Angiama zuwa Oporoma mai tsawon mita 630, da kuma wata sabuwar babbar hanyar shiga birnin Yenagoa.

Tinubu ya yaba wa Gwamna Diri kan yadda yake tafiya tare da tsarin ‘Sabunta Fata’ na Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin jiha da tarayya shi ne sirrin kawo ci gaba cikin hanzari.

Kafin kammala jawabin nasa, Shugaban ya bukaci mahalarta taron da su yi shiru na tsawon minti guda domin karrama sojojin da suka riga mu gidan gaskiya da kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, marigayi DSP Alamieyeseigha.

A nasa jawabin, Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa goyon bayan da gwamnatin tarayya ta ba shi ne ya ba jihar damar kammala ayyukan wutar lantarkin, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci da inganta rayuwar al’ummar jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata