Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu a mukamin sabon shugaban hukumar PTDF da ke lura da rarar man fetur, tare da sabunta wa’adin mulkin Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz a matsayin shugaban kamfanin Transmission Company of Nigeria (TCN).
A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Farfesa Aliyu ya maye gurbin Ahmed Galadima Aminu, wanda ya yi murabus domin tsayawa takarar gwamna a jihar Adamawa a zaben 2027.
Sanarwar ta kara da cewa nadin da kuma sabunta wa’adin mukaman sun fara aiki nan take, inda shugaban kasa ya bayyana cewa hakan na daga cikin kokarinsa na karfafa manyan cibiyoyin makamashi da wutar lantarki a kasar.
Kafin nadin nasa, Farfesa Aliyu shi ne shugaban Hukumar Ilimin Manya, kuma ana kallonsa a matsayin kwararren malami kuma gogaggen masanin harkar gudanarwa. Shugaban kasa na sa ran zai yi amfani da kwarewarsa wajen bunkasa PTDF, musamman a bangaren horas da ma’aikata da kirkire-kirkire a harkar mai da iskar gas.
Hakazalika, an sabunta wa’adin Injiniya Abdulaziz ne bayan tantance yadda ya jagoranci cibiyar wutar lantarki, inda aka samu ci gaba a daidaiton wutar lantarki, fadada hanyoyin rarraba lantarki, da kuma sabunta tsarin aiki, lamarin da ya kara karfafa rawar da TCN ke takawa a harkar wutar lantarki ta Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin biyu da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, kwarewa da kishin kasa, domin cimma manufofin shirin gwamnati na Renewed Hope Agenda.
