Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiTinubu zai ba da tallafin karatu a Nijeriya ga daliban yankin Karebiyan

Tinubu zai ba da tallafin karatu a Nijeriya ga daliban yankin Karebiyan

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da bayar da tallafin karatu ga daliban kungiyar kasashen gabashin Karebiyan OECS don yin karatu a jami’o’in Najeriya, daga shekara mai zuwa.

A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Gros Islet a ranar Litinin tare da Firayim Ministan Saint Lucian Philip J. Pierre, Shugaba Tinubu ya ce tuni aka fara shirin kuma za a aiwatar da shi a karkashin wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasashe mambobin kungiyar OECS.

Ya kuma tabbatar da cewa suna ci gaba da tattaunawa kan bai wa jami’an diflomasiyya daga kasashen OECS izinin shiga Nijeriya ba tare da biza ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata