Sunday, April 5, 2026
HomeWasanniTinubu zai karɓi tawagar Super Falcons a fadar Villa bayan lashe kofin...

Tinubu zai karɓi tawagar Super Falcons a fadar Villa bayan lashe kofin Afirka na mata WAFCON

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai karɓi ‘yan wasan Super Falcons a fadar Aso Villa, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin Afirka ta Mata ta 2024 WAPCON.

Super Falcons sun lashe kofin karo na 10 bayan da suka doke ƙasar Morocco mai masaukin baki, a wasan ƙarshe da aka buga a Rabat.

Tuni Gwamnonin Nijeriya; Uba Sani na Kaduna, da AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, da Hope Uzodimma na jihar Imo, tare da ministocin tarayya, sun tarbi tawagar a filin jirgin saman Abuja domin nuna farin ciki da yabo ga nasararsu.

Haka kuma, ‘yan wasan Falcons hudu -Rasheedat Ajibade, Esther Okoronkwo, Michelle Alozie da Chiamaka Nnadozie, sun shiga cikin Best XI na gasar, inda CAF ta bayyana su a matsayin fitattun ‘yan wasa. Ajibade ce aka zaɓa a matsayin Mafi Kyawun ‘Yar Wasa a gasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata