Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaTinubu zai magance matsalolin Najeriya kafin ya sauka a mulki - Hon....

Tinubu zai magance matsalolin Najeriya kafin ya sauka a mulki – Hon. Abejide

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Yagba Gabas, Yagba Yamma da Mopamuro, Leke Abejide, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai wuce tsammanin jama’a tare da magance matsalolin kasar kafin karshen wa’adinsa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Abejide ya yi wannan bayani ne lokacin da ya karɓi tawagar Renewed Hope Ambassadors a ofishinsa ranar Laraba.

Tawagar ta samu jagorancin Abbas Mustapha, Koodinetan Kasa, da kuma Mustapha Alfa Makanta, Sakatarenta na Kasa.

Kungiyar ta bayyana cewa ziyarar ta zama wani bangare na tuntuba da tattaunawa da shugabanni da suka nuna goyon baya ga manufofin gwamnatin shugaba Tinubu.

Haka kuma sun jaddada cewa duk da kasancewarsa dan jam’iyyar ADC, Abejide ya nuna bajinta wajen fifita ci gaban kasa a kan banbancin jam’iyya, tare da mara wa manufofin Tinubu baya domin tabbatar da sauyi na gari a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata