Monday, April 6, 2026
HomeKetareTrump na shan caccaka bayan wallafa hotonsa a matsayin Fafaroma ta hanyar...

Trump na shan caccaka bayan wallafa hotonsa a matsayin Fafaroma ta hanyar AI” Channels TV

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya wallafa wani hoto da aka kirkira ta hanyar fasahar (AI), yana sanye da kayan Fafaroma a shafinsa na Truth Social, a ranar Juma’a. Wannan na zuwa ne kwana kadan bayan wani kalaman barkwanci da ya yi cewa babban burinsa shine zama Fafaaroma.

A cikin hoton, Trump yana sanye da doguwar rigar Fafaroma, sarkar zinariya rataye a wuyansa, da kuma hular miter, tare da kuma da daga ‘yar manuniyar yatsansa na dama yana nuna sama, lamari ya biyo bayan rasuwar Fafaroma Francis a ranar 21 ga Afrilu, inda ake sa ran fara zaman zaɓen sabon Fafaroma ranar 7 ga Mayu a Vatican.

Inda Cardinal-cardinal za su fara zaman sirri a Sistine Chapel a ranar 7 ga Mayu domin zaben sabon Fafaroma.
A yayin da yake magana da manema labarai a makon nan, Trump ya ce: “Ina so in zama Fafaroma – shi ne burina na farko.”

Kungiyar Katolika ta jihar New York ta bayyana rashin jin dadinta dangane da wannan hoto, tana mai cewa: “Babu abin dariya a cikin wannan hoto. Kada a yi mana ba’a, muna cikin wani lokaci na kunci da ibada.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata