Shugaban Amurka Donald Trump zai tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin na Rasha a yau litinin a wani bangare na kokarin kawo karshen yakin Ukraine da Rasha.
A lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka Trump ya sha alwashin dakatar da rikicin tun a ranar da ya hau kan karagar mulki, amma saboda bin tsarin diflomasiyya ya zuwa yanzu bai kai ga cimma burin nasa ba.
Tawagar kasashen Rasha da Ukraine sun yi zama a birnin Istanbul na Turkiya a makon daya gabata a karon farko cikin kusan shekaru uku, amma tattaunawar ta kare ba tare da tsagaita wuta ba.
