Monday, April 6, 2026
HomeWasanniTsangwama da barazana sun sa iyalan alkalin wasa a gasar firimiyar Ingila...

Tsangwama da barazana sun sa iyalan alkalin wasa a gasar firimiyar Ingila daina zuwa kallo

Alkalin wasa a gasar firimiyar Ingila, Anthony Taylor, ya bayyana cewa iyalinsa ba sa halartar wasanninsa saboda cin zarafi da barazanar da yake fuskanta a cikin filaye da wajen su.

Taylor, wanda ya shafe kusan shekaru 15 yana alkalancin wasanni a matakin ƙoli, ya ce tsananin matsin lamba da ƙiyayya daga magoya baya da masu horaswa ya sa ya fara tambayar kansa ko aikin na da daraja.

Hakazalika, halin “dole sai an ci” da ya yi katutu a kwallon kafa yana cutar da lafiyar kwakwalwa da kwarin gwiwar masu alkalai.

Taylor ya kuma tuna yadda tsohon kocin Roma, Jose Mourinho, ya ci mutuncinsa bayan ƙungiyarsa ta sha kashi a wasan ƙarshe na Europa League a 2023, lamarin da ya sa UEFA ta dakatar da Mourinho daga wasanni hudu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata