Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiTsohon ɗan wasan Barcelona Perez, ya samu rauni a al'aurarsa sakamakon cizon...

Tsohon ɗan wasan Barcelona Perez, ya samu rauni a al’aurarsa sakamakon cizon kare

Tsohon ɗan wasan gaba na Barcelona, Carles Perez mai shekaru 27, na ci gaba da neman lafiyarsa biyo bayan da kare ya cije shi a gabansa.

Rahotanni sun bayyana cewa ya samu raunin ne yayin da yake ƙoƙarin raba karensa da wani kare a lokacin da suka fara faɗa.

Jaridar The Mirror ta ruwaito cewa an kai shi wani asibiti mai zaman kansa da ke Panorama a kusa da garin Thessaloniki, inda aka yi masa dinki har guda shida a wurin da karen ya cije shi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata