Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaTsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP a Ondo ya fice daga...

Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Ondo ya fice daga jam’iyyar

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Ondo Olugbenga Edema, na jam’iyyar NNPP, ya fice daga jam’iyyar.

Edema ya mika wasikar barin jam’iyyar ga shugaban jam’iyyar na gundumar Mahin 11, a karamar hukumar Ilaje ta jihar, tare da mika wa manema labarai ranar Lahadi a Okitipupa.

A cikin wasikar ya koka da rikicin cikin gida da ake fama da shi a jam’iyyar wanda a cewarsa bai dace ga duk wata jam’iyya da ke shirin lashe zabe ba.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan Mayu 9, 2025, ya kuma ce ayyukan shugabancin jam’iyyar sun saba wa ka’idojin jam’iyyun siyasa, Kuma wannan ne dalilin ficewar sa daga jam’iyyar NNPP.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata