Tsohon Sanatan Jigawa ta Tsakiya, Sabo Muhammad Nakudu, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC, tare da wasu manyan ‘yan siyasa a jihar Jigawa.
Nakudu ya ce sun dauki wannan mataki ne domin samun wata jam’iyya da ke bai wa talakawa muhimmanci da kuma inganta dimokuradiyya a cikin gida.
