Tsohuwar Firaministar ƙasar Bangladesh Begum Khaleda Zia ta rasu da safiyar Talatan nan tana da shekaru 80 kamar yadda jam’iyyarta ta Bangladesh Nationalist Party BNP ta sanar.
Jam’iyyar BNP ta bayyana cewa Khaleda Zia ta rasu ne da misalin karfe 6:00 na safe jim kaɗan bayan kammala sallar Asuba a wani asibiti da ke birnin Dhaka, babban birnin ƙasar Bangladesh.
Marigayiyar ta shafe shekaru tana fama da matsananciyar rashin lafiya tare da zaman gidan yari, sai dai duk da haka, a watan Nuwamba da ya gabata ta bayyana aniyarta ta shiga yakin neman zaben da aka shirya yi a Fabrairun 2026, wanda zai kasance zaɓe na farko tun bayan kifar da tsohuwar abokiyar hamayyarta Firaminista Sheikh Hasina a bara.
