Monday, April 6, 2026
HomeKetareUngulai sama da 120 sun mutu bayan sun ci gawar wata giwa...

Ungulai sama da 120 sun mutu bayan sun ci gawar wata giwa a Afirka ta Kudu

Fiye da ungulai 120 sun mutu bayan sun ci gawar giwar da ake zargin masu farauta da sun ba guba a Afirka ta Kudu, a cewar jami’an kula da namun daji.

Wasu ungulan 84 kuma an kwashe su da mota da kuma jirgin sama domin kula da su da kuma duba lafiyarsu bayan faruwar wannan lamari a farkon makon nan.

Wannan shi ne mafi girman guba da aka taba samu tun 2019, lokacin da fiye da 500 suka mutu a Botswana bayan cin gawar giwaye da masu farauta suka saka wa guba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata