Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiUwargidar shugaban Nijeriya ta ba da tallafin naira miliyan 110 ga iyalan...

Uwargidar shugaban Nijeriya ta ba da tallafin naira miliyan 110 ga iyalan ‘yan wasan Kano da suka rasu a hatsari

Uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da tallafin Naira miliyan 110 ga iyalan ‘yan wasan Kano 22 da suka rasu a mummunan hatsarin mota a watan Mayu.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce kowane iyali ya samu Naira miliyan 5 ta hannun Victim Support Fund, wani shiri na gwamnati da ke taimaka wa waɗanda suka shiga cikin bala’i da matsanancin hali.

Fadar shugaban ƙasa ta ce wannan taimako na cikin shirin gidauniyar Renewed Hope na shugaban ƙasa Bola Tinubu, tare da nuna tausayawa da kulawa daga tsagin jagoranci.

‘Yan wasan sun rasu ne a kan hanyar Kano–Kaduna yayin dawowa daga gasar National Sports Festival a jihar Ogun.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata