Wani jirgin kasa ya buge garken giwaye a yankin arewa maso gabashin Indiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar giwaye bakwai nan take, kamar yadda jami’ai a kasar suka sanar a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke tafiya a kan layin dogo, inda giwayen suka tsallaka hanyar, abin da ya haifar da faruwar lamarin, a cewar jami’an gwamnatin kasar.
Jami’an sun ce ana gudanar da bincike domin gano dalilin hatsarin, tare da duba matakan kare dabbobin daji a yankin, musamman a wuraren da layin dogo ke ratsawa kusa da gandun daji.
