Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiWani magidanci ya yanke jiki ya fadi saboda jin matarsa ta haifi...

Wani magidanci ya yanke jiki ya fadi saboda jin matarsa ta haifi ‘yan uku a Kogi

Wani magidanci mai suna Adamu Muhammed Tenimu ya fadi ya suma a asibitin koyarwa ta jami’ar tarayya dake Lokoja a jihar Kogi, bayan samun labarin cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya uku.

Shaidun gani da ido sun ce mutumin da ya ji cewa matarsa ta haifi ‘ya’ya uku, dukkansu ‘yan mata, sai ya fada shauki kuma nan take aka ga ya fadi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Jami’an asibitin sun yi gaggawar kai masa agaji, bayan ya farfado aka sanar da shi uwar da ‘ya’yanta uku suna cikin koshin lafiya.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan farfaɗowa, Muhammed ya bayyana cewa farin ciki da tunanin rashin iya daukar nauyin da ya rataya a wuyansa na kula da yaran, shine ya sa ya yanke jiki ya fadi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata