Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiWani masanin tsaro a Nijeriya ya bukaci a sanya na'urorin CCTV a...

Wani masanin tsaro a Nijeriya ya bukaci a sanya na’urorin CCTV a duk gidajen yari na kasar

Masanin tsaro a Nijeriya Mr. Dickson Osajie, ya bukaci hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta sanya na’urorin CCTV a duk gidajen yari na Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan tserewar fursunoni 16 daga gidan yari na Keffi, a jihar Nasarawa da ke yankin tsakiyar Najeriya.

A wata hira da gidan talabijin na Channels, Osajie ya ce CCTV na hana aikata laifi kuma ya kamata a samu dakunan kula da tsaro da ke sa ido kai tsaye kan abin da ke faruwa.

Ya tambayi yadda ake samun rahotannin tserewar fursinoni daga gidajen gyaran hali yayin da jami’ai ke bakin aiki, yana mai cewa hakan na nuna an karya tsarin tsaro, don haka akwai bukatar a sake inganta shi ta hanyar amfani da fasahar zamani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata