Wani matashi mai shekaru 27, Kabiru Nuhu, ya shiga hannun ‘yan sanda a Jihar Jigawa bisa zargin hallaka mahaifinsa mai shekaru 60 har lahira a ƙaramar hukumar Kazaure.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya zuba mai kamar fetur a jikin mahaifin nasa kafin ya banka masa wuta a unguwar Magama da ke garin Kazaure da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar ranar 1 ga Afrilu, 2026.
Ya ce an garzaya da wanda aka yi ajalin asibiti, amma ya rasu yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa, amma an kama wanda ake zargin dauke da raunukan konewa a jikinsa.
Rundunar ‘yan sanda ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da shirin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Yahaya, ya yi Allah-wadai da lamarin tare da kira ga jama’a su rika warware rikice-rikice cikin lumana.
