Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiWasu jami'an DSS sun fara kamun kafa don a sanya su rakiyar...

Wasu jami’an DSS sun fara kamun kafa don a sanya su rakiyar manya wato VIPs a Nijeriya – Rahoton jaridar Punch

Biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye ’yan sandan da ke tsaron manyan mutane, wasu jami’an hukumar farin kaya ta DSS sun fara neman manyan ’yan Nijeriya domin a ɗauke su a matsayin masu tsaro na sirri, kamar yadda Saturday PUNCH ta ruwaito.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin janyewar ne a ranar 24 ga Nuwamba, a wani yunkuri na mayar da jami’an tsaro kan aikin kare al’umma, musamman ganin karuwar garkuwa da mutane a jihohin Arewa. Daga baya, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an janye jami’ai 11,566 daga ayyukan tsaron VIP.

Rahotanni sun nuna cewa bayan wannan mataki, manyan mutane sun fara tuntubar NSCDC da kamfanonin tsaro masu zaman kansu. Sai dai an gano cewa wasu jami’an DSS suna kai ziyara a asirce ga wasu fitattun mutane, suna roƙonsu su nemi daraktocin DSS na jihohi a tura su matsayin sabbin masu tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata