DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiWasu mahara sun sace mutum hudu 'yan gida daya a jihar Kaduna

Wasu mahara sun sace mutum hudu ‘yan gida daya a jihar Kaduna

 

Al’ummar yankin Keke A dake rukunin gidajen Kaduna Millennium City sun shiga firgici, bayan sace wani yaro dan shekaru biyu tare da ‘yan uwansa mata uku da wasu ‘yan ta’adda suka yi.
An ruwaito cewa, matan wadanda aka sace ‘yan shekaru 9, da 12, da kuma 15 ne, kuma daya daga cikinsu marainiya ce. kamar yadda mahaifin yaran Yunusa Sarkin Samarin Keke ya shaidawa jaridar Dailytrust.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Talata, lokacin da mahaifin yaran ya tafi asibiti domin duba mahaifiyar yaran wadda ke kwance a asibiti.
Duk kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mansur Hassan hakan ya ci tura, kuma bai mayar da sakon waya da aka tura masa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata