Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiWasu tsoffin hafsoshin sojin Nijeriya sun goyi bayan bukatar ayyana dokar ta...

Wasu tsoffin hafsoshin sojin Nijeriya sun goyi bayan bukatar ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaro

Wasu tsofaffin hafsoshin tsaron sun goyi bayan kiran da tsohon hafsan tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor mai ritaya ya yi, na gwamnati ta ayyana dokar ta-baci domin magance ayyukan ta’addanci.

 

A cikin littafinsa mai taken “Scars: Nigeria’s Journey and The Boko Haram Conundrum” ya bayyana cewa rashin mayar da hankali ne ya kawo nakasu wajen yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa Maso Gabashin kasar inda ya bukaci a kafa dokar ta-baci.

 

Haka kuma ya ce samun goyon bayan majalisar dattawa zai taimaka wajen kawo karshen matsalar ta tsaro.

 

Janar Lucky Irabor (mai ritaya), wanda ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaron ƙasa a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatin wancan lokaci ba ta da kayan aikin da za su ba ta damar ayyana dokar ta-baci domin yaƙi kai tsaye da ayyukan ‘yan bindiga a Arewa Maso Gabas.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata