Wasu ‘yan Kenya bakwai sun tabbatar wa da wata kotun Landan shaidar cewa iyayensu ‘yan Burtaniya ne bayan gabatar da gwajin kwayar halitta.
Bayanai daga gwajin sun nuna cewa wasu sojojin Burtaniya shida da ke sansanin horas da soji a Kenya sai kuma wani dan kwangila guda ne iyayen mutanen.
DW Africa ta ruwaito cewa wannan ne karo na farko da wata kotu a Birtaniya ta amince tare da yanke irin wannan hukuncin, wanda hakan ya bai wa mutanen damar neman takardun zama ‘yan kasar.
