Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiWatanni kusan 8 ba a sake jin duriyar mataimakin gwamnan jihar Taraba...

Watanni kusan 8 ba a sake jin duriyar mataimakin gwamnan jihar Taraba ba, in ji rahoton jaridar Daily Trust

Ana tunkarar shekara guda a jihar Taraba, shiru babu amo babu labarin inda mataimakin gwamnan jihar Aminu Alkali.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito watanni takwas kenan ba a ga mataimakin gwamnan jihar Alhaji Aminu Alkali ba bisa rashin lafiya, da hakan ya janyo cece-kuce a kan ci gaba da zamansa mataimakin gwamna ba tare da samun damar gudanar da aikinsa a matsayinsa na biyu a jihar.

Sama da watanni takwas mataimakin gwamnan bai bayyana a bainar jama’a ba bayan ya yi fama da rashin lafiya a bara. An kwantar da shi a Asibiti a Abuja, daga bisani kuma aka garzaya da shi kasar Egypt a lokacin da rashin lafiyarsa ta tsananta.

Gwamnan jihar Agbu Kefas ya kasance yana tafiyar da jihar ba tare da wani mataimaki na kwarai ba wanda ayyukansa suka hada da rike mukamin gwamna idan gwamnan ya samu hutu ko kuma ya kasa gudanar da ayyukansa.

Dadewar Alhaji Aminu yana fama da rashin lafiya ya sanya ayar tambaya kan ko har yanzu zai iya ci gaba da zama a matsayinsa ko kuma a tsige shi.

Sai dai majalisar zartaswar jihar wadda ke da hurumin bayyanawa a kan lamarin ta yi shiru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata