Wednesday, April 8, 2026
HomeSiyasaWike ya fadi dalilan da za su sa Tinubu zai kayar da...

Wike ya fadi dalilan da za su sa Tinubu zai kayar da PDP

Ministan babban birnin Nijeriya Nyesom Wike, ya bayyana cewa jam’iyyarsa, wato PDP, ba za ta iya samun nasarar lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027 ba idan har ba ta sauya tsarin rabon mukamai ‘zoning’ nata ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai, inda ya nuna rashin bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar dangane da tsarin rabon shugabancin jam’iyya da kuma takarar shugaban kasa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP, Adolphus Wabara, ya karbi tsoffin gwamnoni Samuel Ortom na Jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da wasu mutum 38 cikin Kwamitin Amintattu na jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata