Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiWike ya yi martani ga masu sukar kashe Naira biliyan 39 don...

Wike ya yi martani ga masu sukar kashe Naira biliyan 39 don gyara dakin taro na kasa da kasa

Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya kare aikin da yayi na zunzurutun kudi har biliyan 39 wajen gyaran dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.

Ministan, ke jawabi a yayin kaddamar da wata sabuwar hanyar a Abuja, ya ce komai sai da aka canza a cikin dakin taron in ban da gini.

Wike ya ce duk da cewa an kashe Naira Milyan 240 wajen gina dakin taron a shekarar 1991, amma yanzu an samu sauyi sosai a farashin kayayyaki, wanda ya sa aka kashe Naira Bilyan 39 wajen gyaran dakin taron na kasa da kasa.

Ministan Abuja ya ce wadanda ke suka kan yawan kudaden da aka kashe ba su san abinda suke yi ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata