Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi kira da a sauya salon zaben shugabannin Nijeriya, inda ya bukaci ‘yan kasar da su ba da fifiko, wajen zabar masu halaye na gari, da masu tausayi.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X,inda ya ce jagoranci yana samun nasara ko kuma akasin haka,idan aka samu rashin sa’a wajen zaben shugabanni.
Ya nanata cewa ya dade yana magana cewa sanya kabilanci da addini wajen zaben shugabanni ya yi wa kasar illa sosai.
