Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiYahaya Bello ya kulle kofa da cikon mata ta hudu a auren...

Yahaya Bello ya kulle kofa da cikon mata ta hudu a auren da aka daura a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya auri mata cikon ta huɗu mai suna Hiqma, a wani bikin sirri da aka gudanar a karshen mako a birnin Abuja.

Bikin auren, wanda aka shirya cikin ruwan sanyi, ya samu halartar ‘yan Uwa da abokin arziki na kusa da tsohon gwamnan.

Matar sa ta uku, Hafiza Yahaya Bello ce, ta tabbatar da sabon auren a sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta bayyana gamsuwa da shigowar sabuwar amaryar tare da yi mata maraba da fatan alheri.

Yahaya Bello, wanda ya mulki Jihar Kogi daga shekarar 2016 zuwa 2023 karkashin jam’iyyar APC, ya kulle kofar aure, da matansa hudu Amina Oyiza Bello, Rashida Yahaya Bello, Hafiza Yahaya Bello sai sabuwar amaryar, Hiqma.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata