Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga 45 sun sheka lahira a hannun dakarun hadin gwiwar sojin...

‘Yan bindiga 45 sun sheka lahira a hannun dakarun hadin gwiwar sojin Nijeriya a jihar Neja

Dakarun sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an DSS da wasu ‘yan sa-kai, sun yi ajalin ‘yan bindiga 45 da suka kai hari garin Iburu a karamar hukumar Shiroro, Jihar Neja da yammacin Juma’a.

Bayanan sirri daga DSS sun gano cewa ‘yan ta’addan na tafe da babura da dama domin kai hari a yankin, lamarin da ya sa aka sanar da sojoji da ke shirin dakile barazanar.

Bayan sauran bayanai daga mazauna yankin, an ce sun kirga akalla gawarwaki 40 na ‘yan bindigar da kuma babura da dama da aka kone a fafatawar.

A yayin artabun, ‘yan sa-kai biyu sun rasa rayukansu, yayin da hudu ke jinya a babban asibitin jiya na jihar sakamakon harbin bindiga kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata