Monday, April 6, 2026
HomeLabarai‘Yan Bindiga sun afka Kauyen, Tadurga a karamar hukumar Zuru ta jihar...

‘Yan Bindiga sun afka Kauyen, Tadurga a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi 

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tadurga a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi a daren Litinin, inda suka kashe mutane, suka yi garkuwa da wasu, tare da sace dabbobi da kayayyaki.

Wani mazaunin kauyen, Audu Sule, ya ce maharan sun rika harbi ba kakkautawa, yayin da wani, Abdullah Zuru, ya ce harin ya faru ne bayan wani dan lokaci na zaman lafiya da ya bai wa manoma damar girbi.

Gidan talabijin na Channels ya ce, har zuwa hada rahoton hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka kashe ko aka sace ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata