Monday, April 6, 2026
HomeLabarai‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar Niger.

Mazauna yankin sun ce harin farko ya faru ne da misalin karfe 3:00 na asubahin ranar 14 ga Fabrairu a Tugan-Makeri, inda aka mutane 6 suka rasa rayukansu, aka kona gidaje tare da sace wasu. Daga baya da misalin karfe 6:00 na safe, maharan sun kai farmaki Konsoko da Pissa inda aka ce an hallaka karin mutane 26.

Wani mazaunin yankin, Hassan Abdullahi, ya shaida cewa ’yan bindigar sun kai sama da 200 kuma sun shafe awanni suna cin karensu babu babbaka, daga karfe 6:00 na safe zuwa kusan 10:00 na safe.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin Tugan-Makeri da mutuwar mutum shida, yana mai cewa jami’an tsaro sun bazama yankin domin daukar mataki da ceto wadanda aka sace, yayin da cikakken bayani kan sauran hare-haren ke jiran tabbaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata