Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga sun sace mata 20 a wani sabon hari a jihar...

‘Yan bindiga sun sace mata 20 a wani sabon hari a jihar Zamfara

A kalla mata da ‘yan mata 20 ne ‘yan bindiga suka sace a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, yayin da suke neman itace a wajen gari a ranar Asabar.

Wani mazaunin yankin, Sufyanu Moriki, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, yana mai cewa har yanzu masu garkuwar ba su nemi kudin fansa ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya ce hukumar su ba ta samu bayani kan lamarin ba tukuna.

Rahotanni sun bayyana cewa hadin gwiwar ‘yan ta’adda da mayaka ma su da’awar jihadi na kungiyar Lakurawa a yankin na kara dagula lamarin tsaro a Arewacin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata