Wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin mutum biyar, ciki har da jami’an ‘yan sanda biyu da fararen hula uku, a wani hari da suka kai yankin Yarkatsinan Laka da ke ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun kai harin ne ɗauke da makamai masu ƙarfi, a sama da babura 50.
Sanarwar ta ce rundunar ‘yan sanda ta musamman (Strike Unit) ta gaggauta mayar da martani, inda suka yi artabu da maharan, lamarin da ya kai ga shafe ‘yan bindiga 11 a doron duniya, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka.
Sai dai, sanarwar da jaridar Daily Trust ta ambato ta tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda biyu da fararen hula uku sun rasa rayukansu yayin musayar wuta, yayin da wani jami’in ɗan sanda guda ya jikkata, kuma yana karɓar magani inda ake samun sauƙi.
Rundunar ta ce an dawo da zaman lafiya a yankin bayan harin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ahmad Muhammad Bello, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa tsaro domin dawo da cikakken zaman lafiya.
Sa’annan Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba da sahihan bayanai a kan lokaci domin inganta tsaro.
