Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Lanta, Tunga da Bagna da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, inda suka yi ajalin mutane uku tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya tilasta mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa harin ya fara ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Bagna, wanda shi ne garin tsohon kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar, Emmanuel Umar, kafin ya bazu zuwa wasu ƙauyukan makwabta.
Majiyoyi daga yankin sun ce maharan sun iso da yawa a kan babura, inda suka yi ta kai hari na tsawon sa’o’i a yankin.
